Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka
May 6, 2022Jaridun na Jamus sun yi nazari kan kasar Somaliya, inda aka samu mummunan harin ta’addanci. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce bayan samun lafawar rikicin kasar Somaliya, a wannan mako an samu mummunan harin Kungiyar Al-Shabab wanda ya hallaka sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Somaliya. Jaridar ta kara da cewa wannan harin ya kara tabbatar da hatsarin da Somaliya ke da shi duk da lafawar tashin hankali a 'yan shekarun nan. Harin na Al-shabab kan sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya, ya hallaka sojoji goma tare da raunata wasu kimanin ashirin da biyar. A bangarensu ma Al-shabab ta ce, sojoji 170 aka hallaka ba wai goma kawai ba.
Ita kuwa jaridar Tageszeitung ta sake leka kasar Sudan, inda ta ce wai shin yakin basasa na neman dawowa a Darfur ne? Sai Jaridar ta ci gaba da cewa, wani mummunan farmaki da aka kai a yankin Darfur ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Wannan ya kara tada hankalin jama’ar yankin dama kungiyoyin kare hakkin jama’a domin suna masu cewa, tun bayan da sojojin kasar Sudan suka dare mulki bayan kifar da gwamnatin Oumar Albashir, ake ta yawaitar samun hare hare-hare a yankin, wanda ya zama tsakiyar tashin hankali mafi muni a shekarun baya.
Jaridar Die Tageszeitung ce ke dauke da labarinmu na gaba, inda ta duba fadadar baraka tsakanin kasar Mali da Faransa, jaridar ta ce Mali na bukatar daukacin sojan Faransa su fice mata daga cikin kasarta. Inda yanzu gwamnatin kasar Mali ta yanke shawarar soke dukkan yarjejeniyar tsaro da ta soja da ke tsakaninsu da Faransa, wanda ke nufin duk sojan Faransa da ke Mali dole ya fice. Mali ta ce bata bukatar Faransa a yaki da ta‘addancin da yanzu haka ake yi a Mali, kasar ta bada hujjar cewa sun samu sojan Faransa da aikita laifunkan karkashin yaki da ta’addanci da suke yi a cikin kasar Mali, don haka Mali ta ce sun umarci sojan na Faransa da su fice nan take.
Jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba labari mai dadin ji a bangaren 'yan fashin teku. Jaridar tana mai cewa, wannan ma dai yanzu ya sa har wasu kasashen yamma da suka tura dakaru a yankin, sun sanar da kawo karshen aiki, inda misali gwamnatin Jamus ta ce aikin rundunar sojan ruwanta a gabar ruwan Somaliya ya zo karshe, domin yanzu kusan an manta lokacin da aka ji duriyar batun fashi kan teku a gabashin Afirka. A shekarun baya dai gabar ruwan Somaliya ta kasance mafi hatsari da yawan 'yan fashin teku a duniya.