Japan ta cika shekaru biyar da afkuwar bala'in Tsunami
March 11, 2016Talla
Yayin bikin a birnin Rikuzentakata an yi shuru na tsahon minti guda domin tunawa da mutane 18,000 din da suka rasa rayukansu yayin bala'in na Tsunami da ya afku a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2011.
A ranar biyar ga watan Satumba na bara ne dai aka amince da komawar al'ummar birnin Naraha zuwa gidajensu, a matsayin birni na farko daga cikin bakwai da aka kwashe al'ummominsu sakamakon hadarin makamashin nukiliyar na Tsunami, sai dai watanni shida ke nan har kawo yanzu mazauna birnin 440 daga cikin 7,400 da aka kwashe a baya ne kacal suka koma.