1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'yyar SPD ta lashe zaɓen majalisa a jiha mafi girma

Zainab MohammedMay 13, 2012

Jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha kaye a jiha mafi yawan jama'a ta Nord Rhein Wesphalia. Hakan ya sa ministan muhalli kuma shugaban CDU na jihar yayi murabus daga shugabancinta.

https://p.dw.com/p/14uig
Hannelore Kraft, federal state premier of North-Rhine Westphalia (NRW) and top candidate of the Social Democratic Party (SPD) stands next to her husband Udo and son Jan as she addresses supporters after first exit polls for the NRW federal state election in Duesseldorf May 13, 2012. Chancellor Angela Merkel's conservatives suffered a crushing defeat on Sunday in an election in Germany's most populous state, a result which could embolden the left opposition to step up its criticism of her European austerity policies. REUTERS/Wolfgang Rattay (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Ministan kare muhalli na tarayyar Jamus Norbert Röttgen yayi murabus daga shugabancin jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya na CDU a jihar Nord Rhein Wesphalia, bayan shan kaye da jam'iyyar tayi a zaɓen 'yan majalisa daya gudana a wannan lahadi. Röttgen ya faɗa wa manema labaru a fadar jihar da ke Dusseldorf cewar, sakamakon bayyananne ne, kuma babu wata makawa a kayen da jam'iyyarsa ta CDU tasha. A matsayinshi na shugaban jam'iyyar a jihar data fi yawan al'umma a tarayyar jamus, ministan muhallin ya ce laifinsa ne faɗuwar da jam'iyyarsu tayi, dangane da hakane ya zamanto wajibi yayi murabus daga shugabancinta a jihar.

Ya ce "ni ne fitaccen dan takara, kuma a nawa tunanin yakin neman zabe ya ta'allaka ne akan muhimmancin batutuwan daya kunsa, tsari da yanayin aiwatar dashi. Don haka da farko wannan gazawa ce daga ɓangare na, wanda ya jagoranci faɗuwar jam'iyyata. Sakamakon na nuni da cewar yawancin wakilan CDU ba zasu sake kasancewa a majalisar jihar ba. Wannan abun bakin ciki ne, bawai ga resu kaɗai ba amma ga jam'iyyar baki ɗayanta".

Jihar dai na da yawan al'umma fiye da na ƙasar Holland baki ɗaya, da karfin tattalin arziki daya kai na kasar Turkiyya. Zaɓen dake zuwa watanni 18 gabannin na ƙasa baki ɗaya inda ake saran shugabar gwamnati Angela Merkel zata nemi zarcewa a karo na uku, na da matukar tasiri a fagen siyasar Jamus.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Umaru Aliyu