1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta sanya biyan harajin masallaci

Abdullahi Tanko Bala
December 27, 2018

Shawarar sanya harajin za ta dace da makamancin harajin Coci da Kiristoci ke biya kuma tuni shugabannin musulmi a Jamus din suka amince da ita.

https://p.dw.com/p/3Afgf
Sehitlik Moschee in Berlin
Hoto: Getty Images/C. Koall

Matakin wanda shugabannin musulmi a Jamus suka amince da shi na da nufin mayar da masallatai zama masu dogaro da kansu maimakon dogaro da tallafi daga kasashen waje.

‘Yan majalisar dokoki na kawancen gwamnatin Jamus sun ce suna duba yiwuwar bullo da harajin masallaci ga musulmi kwatankwacin harajin da Kiristoci a Jamus suke biya na kula da Coci.

Thorsten Frei na Jam’iyyar CDU ta Angela Merkel ya shaidawa mujallar Weltdaily cewa harajin masallacin muhimmin mataki ne da zai bai wa masallatai a Jamus damar dogaro da kansu maimakon neman taimako daga kasashen waje wanda ke haifar da damuwa na tasirin kungiyoyi da gwamnatocin kasashen waje na tsattsauran ra’ayi da kuma akidu.

Kiyasi ya nuna akwai musulmi fiye da miliyan hudu da rabi da ke zaune a Jamus.