Kwalliya ba ta biyan kudin sabulu kan dokokin corona a Jamus
December 10, 2020Talla
Alkaluman masu kamuwa da Corona a Jamus na cigaba da daukar hankullan mahukuntan kasar, bayan da suka bayyana cewa dokokin hana yaduwar cutar da ake bi a halin yanzu basa biyan bukata.
Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Markel, ta bukaci da a karfafa dokokin hana yaduwar annobar nan da kamin a fara bukukuwan Kirsimati gadan-gadan, wadanda suka hada da tsawaita hutun 'yan makaranta da kuma rufe wuraren kasuwanci.
Haka zalika cibiyar Robert Koch ta ce alkaluman masu kamuwa da cutar a ko wace rana kan kai kimani 20,000, kamar yadda shugaban cibiyar Lother Wieler ya jinjina lamarin.
Lother Wieler ya ce yanayin yadda ake samun masu kamuwa da cutar ya ta'azzara musamman a 'yan makwannin nan, kawo yanzu lambar na cigaba hauhawa.