1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta tsawaita dokar kulle

January 20, 2021

Gwamnatin Jamus ta tsawaita dokar kulle zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu don dakile yaduwar annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3o8kz
Deutschland Berlin Angela Merkel
Hoto: John MacDougall/AP/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamsu Angela Merkel da shugabanin jihohi 16 sun cimma matsayar ce a wani mataki na dakile yaduwar annobar da ke kara yaduwa a kasar.

Kazalika, shugabannin sun ce ya zama wajibi dukan fasinjoji su ci-gaba da sanya takunkumin fuska kamar yadda aka saba a ababen hawa na haya, da cikin shagunan siyar da kayayyakin amfanin yau da kullum. Ma'aikata kuma za su ci-gaba da yin aiki daga gida a inda ake da bukatar hakan.

Dama dai tuni a watan Nuwanba bara ne kasar ta rufe makarantu da sauran shaguna da gidajen cin abinci da na siyar da barasa da kuma haramta haduwa mutane da dama a wuri guda. 

Adadin masu dauke da cutar corona a Jamus sun karu inda a halin yanzu mutum fiye da miliyan 2 ne suka dauke da ita a kasar yayin da mutum fiye da dubu 47 suka kwanta dama a cewar cibiyar Robert Koch.