Jamus ta taimaki Mali da Euro miliyan ɗaya
November 1, 2012Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya kai ziyarar aiki a ƙasar Mali inda ya gana da hukumomin Bamako game da hanyoyin samar da zaman lafiya.
Westerwelle ya yi amfani da wannan dama, inda ya ba da albishirin tallafin tsabar kuɗi Euro miliyan ɗaya a matsayin agajin Jamus ga al'umar Mali da ta shiga mawuyacin hali sakamakon rikicin da ƙasar ke fama a shi. Jamus ta buƙaci ayi amfani da wannan kuɗaɗe, ta fannin samar da abinci, kiwon lafiya da kuma taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
A ɗaya wajen, Jamus ta yi tayin ba da ɗauki domin ƙwato yankin arewancin Mali da a halin yanzu ke cikin hannun ƙungiyoyi masu tsatsauran kishin addinin Islama.
Asarid Ag Ibarkawane shine mataimakin shugaban Majalisar dokokin Mali na buiyu, ya baiyana mahimmancin dangantaka tsakanin Jamus da Mali:
Jamus itace ƙasar farko da ta amince da samun 'yancin kan ƙasar Mali.Kasashen biyu na da alaƙar ƙut da ƙut.Wannan dama ce muka samu, domin baiyanawa minista Westerwelle inda aka kwana, a yunƙurin warware rikicin ƙasar Mali, sannan mu ji irin tallafin da ƙasarsa ka iya badawa domin cimma burin da aka sa gaba.
Bayan ganawa da hukumomin Mali, a ɗaya wajen Guido Westerwelle ya tattauna da ƙungiyoyin farar hula game da batun aika rundunar ƙasa da ƙasa a yankin arewacin Mali.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammed Abubakar