Jamus ta kammala kwashe sojojinta daga Mali
December 16, 2023
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius wanda ya tarbi sojojin, ya yaba kyawun aikin da suka gudanar yayin da suke cikin runudnar MINUSMA a Mali.
Sama da mayakan na Jamus 300 ne dai ke a rukunin na karshe, daga cikin sama da dubu 20 da yi aikin yaki da ta'addanci a Mali.
Jim kadan bayan kwace iko da gwamnatin farar hula a Malin a 2021 ne dai sojoji suka bukaci dakarun Faransa su fice daga kasar.
Sannan cikin watan Yulin wannan shekarar ne kuma suka bukaci dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su ma fita daga kasar.
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, ya har yanzu Jamus na yankin sai dai a kan wani tsari na daban.
Gwamnatin Malin dai ta kulla danganta da kasar Rasha.
Ministan ya ma ce nan ba da dadewa ba zai kai ziyara a Jamhuriyar Nijar.