1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce mai yiwuwa harin Frankfurt na ta'addanci ne

March 3, 2011

Harin da aka kai a filin jirgin saman Frankfurt da ya hallaka sojojin Amirka biyu, Binciken farko ya nuna alamun harin ta'addanci ne.

https://p.dw.com/p/10TBY
'Yan sanda ke zirga zirga a filin jirgin saman FrankfurtHoto: picture alliance/dpa

Babbar kotun kasar Jamus ta nuna alamun cewa harin birnin Frankfurt da ya hallaka sojin Amirka biyu na da alaka da ayyukan ta'addaci. Idan wannan zargi ya tabbata, wannan shi ne zama karon farko da aka fiskanci harin ta'aadci a tarayyar jamus tun bayan wanda Amirka ta fiskanta shekaru kusan goman da suka gabata. Sojojin saman Amirka guda biyu ne suka mutu, wasu biyu kuma suka samu raunuka bayan da wani dan kosovo mai shekaru 21 da haihuwa mai suna Arid Uka ya bude musu wuta. Kasar ta Jamus inda a nan ne aka kitsa harin da 11 ga watan satumba na New-york, ta saba kawar da duk barzanar harin ta'addaci da aka yi mata a baya.

A halin yanzu ma dai kwararrun 'yan sanda na kasashen na Jamus da kuma Amirka suna ci gaba da gunadar da bincike domin gano musabbabin harin da kuma wande ke da alhakin kai shi. Komishinan da ke kula da harkokin cikin gida na jihar Hesse inda abin ya faru, ya bayyana cewa shi wanda ake zargi da laifin kai harin, wani mai tsautsauran ra'ayin Islama ne. Amma bai bayyana ko ina da alaka da wata kungiya ta 'yan takife ba, koko a'a.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman