Jamus: SPD za ta shiga shirin kafa gwamnati
December 7, 2017Talla
Jagoran jam'iyyar Social Democrats (SPD) a nan Jamus ya bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa 'ya'yan jam'iyyar sun mara baya a tattaunawar da za a yi da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel don kawo karshen kiki-kaka da siyasar kasar ta shiga.
Martin Schulz ya fadawa babban taron na jam'iyyar SPD a birnin Berlin cewa abin da ke da muhimmanci shi ne wace rawa jam'iyyar za ta taka a gwamnati idan aka aje banbanci da ke akwai tsakaninsu da jam'iyyar ta Merkel CDU masu ra'ayin mazan jiya.
A cewar Schulz dai dole kasar ta Jamus ta kara samun karfi lamuranta su inganta wannan shi ne burin jam'iyyar ta SPD.