1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na neman mafita a gwamnatinta

Ramatu Garba Baba
July 1, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za su dauki kwararan matakai na warware matsalar kwarar baki 'yan gudun hijira tare da taimakon gwamnatin hadaka.

https://p.dw.com/p/30d7u
Deutschland Sommerinterview im ZDF mit Angela Merkel
Hoto: picture alliance/dpa/ZDF/J. Detmers

A wata hira da ta yi da kafar talabijin ta ZDF a kasar, Merkel ta yi bayani kan sabanin da aka yi ta samu a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar kawancen CDU da CSU kan 'yan gudun hijirar, sai dai ta ce an kama hanyar magance matsalar don kaucewa rushewar gwamnatin hadakar da aka kulla da kyar. Merkel ta yi karin haske kan batutuwa da dama da suka shafi ci-gaban kasar.

A wannan makon ne Merkel  ta yi nasarar shawo kan lamarin, bayan da ta samu dai-daito da kasashen Turai kan magance matsalar kwararar 'yan gudun hijirar da ya zame ma ta babban kalubale.Yanzu za a soma mayar da 'yan gudun hijirar da suka shigo kasar daga wata kasar Turai cibiyar da aka tanadar musu a yayin da Jamus  ke ci gaba da duba cancantarsu na zama a kasar.

Gwamnatin Merkel dai ta fuskanci tsananin suka tun  bayan da ta amince da bude kofofin kasar ga 'yan gudun hijira fiye da miliyan guda a shekarar 2015.