Kasashe sun dauki alwashin kawo karshen rikicin Libiya
December 29, 2019Talla
Tun da farko an bayyana sanya bakin Jamus da Majalisar Dinkin Duniya a rikicin na Libiya, a matsayin hanya daya tilo da zata kawo karshen rikicin gwamnati da na dakarun janar Khalifa Haftar. A farkon wannan wata na Disamba ne shugaba Putin na Rasha ya yabawa kokarin Jamus na kirkirar matakan da za a bi don zaman lafiya ya samu a kasar. Kasar Libiya dai ta shiga yakin basasa ne bayan hambarar da gwamnatin shugaba Moamer Gaddafi a shekara ta 2011.