1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Karfafa dangantaka da Senegal

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 22, 2022

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci a karfafa dangantakar da ke tsakanin kasarsa da Senegal. Yayin wata ziyarar aiki a Snegal, shugaban kasar Jamus din ya bukaci karfafa huldar da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/47OV9
Shugaban kasar Jamus Steinmeier a Senegal | Shugaba Macky Sall
Shugaban ksar jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Senegal Macky SallHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Frank-Walter Steinmeier ya bayyana hakan ne, yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki uku da yake yi a Senegal din. A nasa bangaren Shugaba Macky Sall na Senegal da ya karbi bakuncin Steinmeier a Dakar babban birnin kasar, ya bukaci Jamus da ka da ta kwashe sojojinta da ke makwabciyar kasa Mali bayan da Faransa ta ayyana kwashe sojojinta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka. Jamus dai na da sojoji dubu daya da 170 a Mali, a wani bangare na rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma tattauna kan allurar riga-kafin corona, inda Shugaba Sall na Senegal ya jaddada cewa Afirka ba ta bukatar sadakar allurar riga-kafin sai dai tana bukatar samun damar samar da riga-kafin da kanta. A nasa bangaren Steinmeier ya nunar da cewa kamfanin Jamus da ke samar da riga-kafin wato BioNTech, na shirin samar da tsarin tafi da gidanka na dakunan harhada magunguna cikin manyan akwatunan Kontaina da zai bai wa Afirkan damar samar da alluran. Steinmeier da ke zaman shugaban kasar Jamus na biyu da ya taba yin ziyarar aiki a Snegal tun bayan Heinrich Lübke da ya kai ziyara a 1962, ya bude sabon ofishin cibiyar Goethe ta Jamus a Dakar fadar gwamnatin kasar ta Senegal yayin ziyarar tasa.