Jamus na shirin kafa dokar hana saka nukabi
August 19, 2016Kasar Jamus na shirin daukar matakin haramta saka tufafin burka da nikabi a wasu guraren taruwar jama'a a kasar. Ministan cikin gidan kasar Thomas De Maiziere ne ya bayyana hakan a karshen wani taro da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta shirya a wannan Jumma'a tare da sauran jam'iyyu abokanin kawancanta.
Wannan mataki da jam'iyyun suka ce za su shigar da bukatar mayar da shi a matsayin doka a wani mataki na kyautata tsaro a kasar zai tanadi haramta saka nikabi da duk wata tufa mai rufe huska a ma'aikatun gwamnati da makarantu da jami'o'i dama a cikin kotuna da sauran guraren taruwar jama'a ko kuma a lokacin tukin mota.
Sai dai ministan bai bayyana wani jadawali na lokacin da za su shigar da wanann doka ba wacce tuni ta fara fuskantar adawa har a bangaren masu ra'ayin mazan jiya ta SPD mai kawance da jam'iyar CDU ta firaminista Angela Merkel.
Tufafin nikabi da burka dai na neman zaman ruwan dare a kasar ta Jamus tun bayan da ta bayar da mafaka da 'yamn gudun hijira sama da miliyan daya kasashen Siriya da Iraki.