1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Matuka jiragen kasa na yajin aiki

Abdoulaye Mamane Amadou
September 2, 2021

Direbobin jiragen kasa a tarayyar Jamus sun shiga wani yajin aiki karo na uku duk da tayin da gwamnatin kasar ta yi masu game da karin kudaden albashi saboda bullar annobar corona.

https://p.dw.com/p/3znkH
Deutschland | Bahnstreik Berlin
Hoto: Annegret Hilse/REUTERS

Kungiyar matuka jiragen kasa a Jamus sun tsunduma sabon yajin aiki karo na uku a yunkurinsu na tilasta wa kamfanin Deutschen Bahn mallakar gwamnatin biyan wasu hakkokinsu duk da sabon tayin da gwamnatin ta yi musu.

Yajin aikin zai shafi harkokin zirga zirgar jama'a, ya zo kwanaki bayan wani makamancinsa da ma'aikatan suka yi a bangaren dakon kaya a fadin tarayyar Jamus.

Kungiyar kwadago ta GDL ta kasa cimma daidaito da hukumomin kasar kan wasu karin kason kudaden albashi sakamakon bullar annobar corona, inda kungiyar ta yi fatali da sabon tayin kamfanin Deutschen Bahn, cewar zai kara adadin da suke bukatar ne kawai a cikin tsukin wasu shekarun da ke tafe.