Jamus: Hadin kai domin yaki da Corona
April 3, 2021Talla
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a sakonsa na zagayowar bukukuwan Ista na wannan shekarar, ya bukaci al'ummar kasar da su mara wa gwamnati baya yayin da take yaki da annobar coronavirus ko COVID-19 zagaye na uku duk kuwa da kuskuren da yace mahukuntan sun yi a baya.
Hakan ba zai rasa nasaba da zanga-zangar da aka gudanar a Stuttgart, ta adawa da matakan yaki da annobar. Haka kuma kungiyar likitoci ta kasar tace ba za ta lamunci nuna wariya wajen bayar da allurar a tsakannin yan kasar ba.