Jimamin tunawa da yakin duniya na farko a Verdun na Faransa
May 29, 2016Bikin jimamin wanda ya samu halartar 'yan Faransa da Jamusawa masu tarin yawa a wajen farfajiyar katafaren guri da ke nuna alamun irin yadda Faransawa da Jamusawa sama da dubu dari suka hallaka.
A yayin jimamin dai Shugaba Angela Merkel ta ce garin Verdun na daya daga cikin yake-yake mafiya muni da Duniya ta taba fuskanta.
Shugabar gwamnatin Jamus din ta kara da cewar:
"Shekaru dari da suka gabata dakarun Faransa dana Jamus sun yi gumurzun fada a nan,to amma duk da haka irin yadda aka karrama ni da nuna min faran- faran a matsayina na shugabar gwamnatin Jamus abin abin na dama ne."
Shima a nasa bangaren shugaban Faransa Francois Hollande ya ce a nan Verdun ne Francois Mitterand da shi da Helmut Kohl suka sha hannu domin karfafa dangantaka a tsakanin su.
Kimanin shekaru dari da suka gabata ne dai dakarun kasashen biyu suka fafata a garin Verdun wanda ya janyo asarar rayuka masu dumbin yawa daga dukkanin bangarorin biyu.