Jamus: CDU ta Merkel ta fadi a zaben Berlin
September 18, 2016Sakamakon farko na zaben yanki a birnin Berlin ya nunar da cewa jam'iyyar SPD ta kasance a sahun gaba bayan da ta samu kashi 23% na kuri'un da aka kada, a yayin da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta zo ta biyu da kashi 18% , jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki na a matsayin ta uku da kashi 11,5%.
Idan dai har wannan sakamako wanda tashar talabijin ta ARD ta bayyana ya tabbata to kuwa wannan shi ne sakamako zabe mafi muni da jam'iyyar ta CDU mai mulki ta taba samu tun bayan hadewar sassan Jamus a shekara ta 1990. Wannan koma baya da jam'iyyar shugabar gwamnatin kasar ta fuskanta a birnin na Berlin ya zo ne makonni biyu bayan da dama ta sha kashi a zaben mecklenburg-pomerania inda ta zo ta uku.
Ana dai fassara wannan koma baya da jam'iyyar CDU take fuskanta da adawa da wasu 'yan kasar ta Jamus ke yi da matakin gwamnatin Angela Merkel na bude kofofin kasar ta Jamus ga baki 'yan gudun hijira kimanin miliyan daya a shekarar da ta gabata. A yanzu dai jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki wacce aka kafa a shekara ta 2013 ta yi nasarar a karo na farko shiga majalisar dokokin birnin na Berlin.