1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Andrea Nahles ta zama sabuwar shugabar SPD

Ramatu Garba Baba
April 23, 2018

Jam'iyyar 'yan gurguzu ta SPD a Jamus ta zabi Andrea Nahles a matsayin shugabar jam'iyyar, ita ce macen farko da ta taba rike wannan mukami a tarihin jam'iyyar.

https://p.dw.com/p/2wTME
Außerordentlicher Bundesparteitag der SPD
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Jam'iyyar 'yan gurguzu ta SPD ta zabi mace a karon farko a tarihinta a matsayin shugaba watau Andrea Nahles a gaban 'yar takara Simonne Lange a babban taro na musammun da jam'iyyar ta kira a jiya Lahadi a Wiesbaden da ke a yammacin Jamus. Wanda ake ganin Andreas Nahles tana da manyan kalubale a gabanta na dinke rarrabuwar kawunan da ke tsakanin ya'yan jam'iyyar tun bayan da jam'iyyar ta yake shawarar shiga gwamnatin kawance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel. Andrea Nahles tsohuwar ministan kwadago a gwamnatin hadaka ta uku ta Jamus ta samu kishi 66,35 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben da wakilai 600 na jam'iyyar suka  halarta a gaban tsohuwar 'yar sanda Simone Lange ita ma mace kana magajin garin Flensburger.

Außerordentlicher Bundesparteitag der SPD
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

 

Andrea Nahles 'yar shearu 47 wacce mahaifinta tsohon magini ne ta taso tun tana da kuriciya tana gwagwarmaya a cikin jam'iyyar ta SPD,daya daga cikin dadun jam'iyyun siyasa na Jamus wacce aka girka tun a shekara ta 1875 sama da shearu 150 ke nan. Tana daga cikin 'yan zafin kai na jam'iyyar wacce a lokacin da take rike da matsayin shugabar matasa na Jam'iyyar watau JUSOS ta kasance daga cikin wadanda suka tayer da kayar baya don nuna adawa ga shugaban jam'iyyar na wacan lokaci Rudolf Scharping.