Jam'iyyar Die Linke ta samu nasara a zaben Thuringia
March 5, 2020Talla
Jamiyyar ta Die Linke ta samu goyon bayan jam'iyyun siyasar na SPD da kuma masu fafutukar kare muhali. Sai dai jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta kauracewa ba da goyon baya ga jam'iyyar ta Die Linke saboda alakar da ta ce ta yi a can baya da jam'iyyar 'yan Nazi. A zaben farko da aka yi a jihar a cikin watan jiya kafin a sake shi, dan takarar jam'iyyar FDP Thomas Kemmerich ya samu nasara da goyon bayan jam'iyyar AFD da kuma CDU abin da ya janyo rikicin siyasa a Jamus din har wanda aka zaban ya yi marabus.