1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam’iyyar SPD ta nada sabon shugaba.

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMw

A nan cikin gida Jamus, jam’iyyar SPD ta gabatad da sabon shugabanta, wanda za a zaba a wani taro na musamman da `yan jam’iyyar za su yi a ran 14 ga wannan watan. Rahotannin da muka samu sun ce jam’iyyar ta gabatad da Matthias Platzeck, Firamiyan jihar Brandenburg ne tamkar wanda zai gaji Franz Münterfering, shugabanta mai barin gado, wanda ya ba da sanarwar yin murabus daga wannan mukamin, ba zato ba tsammani a ran litinin da ta wuce.

Shi dai Müntefering, ya sha kaye ne a wata gwagwarmaya kan madafan iko tsakanin `yan jam’iyyarsa, abin da kuma ya janyo yanke shawarar daukar wannan matakin yin murabus da ya yi. Hakan ne dai kuma ya sa Firamiyan jihar Baveriya kuma shugaban jam’iyyar CSU, Edmond Stoiber, shi ma ya janye daga shiga cikin gwamnatin hadin gwiwar da ke shirin kafawa tsakanin jam’iyyun SPDin da na CDU. A ganin Stoibern dai, gwamnatin ba z ata yi karko ba. Sabili da haka ne ya ke ganin ya fi gwammacewa ya rike mukaminsa na yanzu, tamkar Firamiyar jihar Baveriyan.