Jam'iyyar SPD ta gudanar da babban taronta
December 4, 2011A babban taron ta da ta gudanar a birnin Berlin jam'iyyar SPD ta yi kira da a gaggauta dora haramci akan jam'iyyar NPD mai manufar kyamar baki . A cikin wani kuduri da ta tsayar jam'iyyar ta bukaci yin yaki da akidar nuna wariyar jinsi da kyamar baki tsakanin al'uma tare da mika bukatar ba jama'a kwarin gwiwa da kuma binciken aikin 'yan sanda da jami'an kare kundin tsarin mulki. Shugaban jam'iyyar a majalisar dokoki ta Bundestag, Frank-Walter Steinmeier ya soki gwamnatin gamin gambizar CDU da FDP da ke mulki da yin kafar ungulu ga manufar kasahen Turai ga baki daya. Ya ce Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta nuna halin munafinci yana mai cewa mutun ba zai kara wa kasarsa bashi ba a sakamakon tallafa wa tattalin arzikin wasu kasashe dabam da zai yi. A cikin jawabinsa na bude taron tsohon shugaban gwamnatin Jamus, Helmut Schmidt ya yi kira ga al'umar Jamus da su nuna zumunci wajen tinkalar matsalar ta bashi da ke addabar kasashen Turai . Ya ce Jamus ita ce za ta fi kowace kasa cin gajiyar tafarkin samar da hadin kan kasashen Turai.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal