Jamus: Manyan jam'iyyu na rasa tasiri
October 14, 2018Sakamakon zaben ya nuna jam'iyyar CSU ta rasa gagarumin rinjaye da ta dade tana samu a Jihar Bavaria, kuma ita ce babbar mai kawance da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel, lamarin da ke kara nuna cewa jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki ta yi nasarar shiga majalisar dokoki.
Jam'iyyar CSU da ke kan gaba a sakamakon zabe tana bukatar shiga kawance da wasu jam'iyyu kafin kafa gwamnati ta gaba a jihar da ta fi kowace wajen girman kasa a Jamus. Duk da nasarar shiga majalisar dokoki da AfD ta yi, jam'iyyar CSU ta kawar da yuwuwar shiga kawance da ita kan batun kafa gwamnati, da ake sa ran Markus Soeder zai ci gaba da rike mukamun firimiya na jihar.
Ga abin da Markus Soeder firimiyan jihar ta Bavaria ke cewa kan sakamakon zaben:
"Haka yake wannan rana ba ta zo da sauki ba ga jam'iyyar CSU. Ba mu samu sakamakon mai kyau ba; saboda ba mu samu sakamakon da ya yi mana dadi ba, duk da yake muna jiran sakamakon karshe. Mun amince da sakamakon da zuciya daya kuma za mu yi koyi da abin da ya faru. Za mu yi bitar abin da ya faru karara duk da yake akwai tattaunawa da sharhi, jam'iyyar CSU ba kawai ita ce ta fi karfi ba, amma ta samu sakamakon da za ta iya kafa gwamnati."
Tuni Katrin Ebner-Steiner da ta jagoranci jam'iyyar AfD wadda ta samu shiga majalisar dokokin jihar, ta ce lokaci ya rage kafin su kwace madafun iko daga hannun manyan jam'iyyun siyasar Jamus karkashin kawance shugabar gwamnati Angela Merkel:
"Wannan sakamakon sako ne ga Merkel: Merkel dole ta tafi. Mu ne wadanda za su gaji jam'iyyar CSU; mun tsaya kan al'adunmu, da iyalanmu da kanmu a Bavaria, 'yan uwa Bavaria kasa mai albarka."
Wasu daga cikin masu zabe suna gani haka zai zama darasi ga 'yan siyasa domin dukufa wajen magance matsalolin da ake fuskanta:
"Wasu 'yan siyasa za su sosa keya, saboda da tunanin wannan yanayin abubuwa ba za su ci gaba da tafiya da rashin cika alkawari ba, ba zai dauki lokaci ba za ka iya rasa kuri'un da kake bukata."
"Wannan yana da nasaba da siyasar kasa baki daya, ina gani, shi ya saka CSU ta samu kanta a wannan yanayi. Ina fata kan samun gwamnati mai matsakaicin ra'ayi. Lokaci ya yi da za mu yi rayuwa karkashin gwamnatin hadaka, gwamnati kasa ma haka ake wajen tafiyar da lamura tare da duba abubuwa masu tasiri gami da duba rawar da kowa yake takawa."
Zaben ya nuna cewa kallo zai koma sama kan makomar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kawance da take jagoranta, yayin da masu matsanancin ra'ayin ke kara samun togomashi.