Rikici ya dagule a jam'iyyar APC mai mulkin Nageriya
March 6, 2020Talla
Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki ya ce rikicin cikin gidan da ya barke a cikin jam'iyyar na da ruwa da tsaki da gwagwarmayar mallakin ruhin jam'iyyar domin zaben shekara ta 2023.
A wata Hirar da tashar DW Adams Oshiomhole ya ce wasu gwamnonin jam'iyyar guda uku ne ke jagorancin yunkurin tsige shi da nufin neman damar samun shugabancin kasar a shekara ta 2023.
Shugaban jam'iyyar ya ce baya aiki ga jagoran jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu, kuma ba shi da wani tasiri wajen fitar da dan takara na shugaban kasar jam'iyyar a zaben na gaba.
Wani rikicin cikin gida tsakanin manyan 'ya'yan APC dai ya kalli wasu kotuna guda biyu yanke hukuncin da ya saba a bisa makomar shugaban da ma kila jam'iyyar da ke neman dorawa a cikin babakeren mulki na kasar