1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyya mai mulki Indiya ta fadi a zaben jiha mai tasiri

Suleiman Babayo
December 24, 2019

Jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulkin kasar Indiya ta sha kaye a zaben jihar Jharkhand da ke gabashin kasar a hannun 'yan adawa karkashin jagorancin babbar jam'iyyar adawa ta Congress.

https://p.dw.com/p/3VIaK
Indien Kolkata Proteste gegen Staatsbürgerschaftsrecht
Hoto: picture-alliance/Xinhua/T. Mondal

Jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulkin kasar Indiya ta sha kaye a zaben jihar Jharkhand da ke gabashin kasar a hannun babbar jam'iyyar adawa ta Congress da wdaanda suke kawance. Ita dai jam'iyyar BJP ta masu kishin Hindu ta rasa jihar da take mulka tun shekara ta 2014, abin da ake gani a matsayin gagarumin koma baya ga manufofin Firaminista Narendra Modi.

Jam'iyya mai mulkin Indiya ta rasa zaben jihar a gabashin kasar yayin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar zama dan kasa da majalisar dokokin kasar ta amince da ake gani nuna wariya ga Musulmai. Karkashin sabuwa dokar tsirarun addinai na kasashen makwabtan Indiya za su iya samun takardun zama 'yan kasa bisa dalilan fuskantar musgunawa amma ban da Musulman da suka fito daga kasashen, inda ake ganin akwai wasu mabiya dariku na Musulmai tsiraru daga kasashen wadanda Indiya ta kawar da ido kansu.