Jam´iyar SPD a Jamus ta kammalla zaman taron ta na kasa
November 16, 2005Jam´iyar SPD ta nan Jamus, ta kammalla zaman taron ta na kasa, a yau laraba, taron da ta fara ranar litinin da ta wuce, a Karlsruhe dake kudu maso yamma.
Saban shugaban jam´iyar Mattias Platzeck, da ya ke bayyanin rufe taron, yace SPD da a halin yanzu ta kulla kawace da CDU, a gwamnatin hadin gambiza, ta yi alkawarin dukkufa aiki ka´in da na´in domin ci gaba kasa, da kuma daukaka tagomashin Jamus a fagen diplomatia na dunia.
Ya ce a shire ya ke ya kara karfafa mutunci Jamus da kuma sunan da ta yi, na kare yanci, adalci, da taimakon jama´a, na ci da na wajen kasar.
Ranar buda taron wakilan SPD daga jihohin kasar baki daya sun kada kuri´ar amincewa da yarjejeniryar da a ka cimma, ta kaffa gwamnati, tsakanin SPD da CDU.
Bayan kwanaki 3 na mahaurori,wakilan sun yanke shawara sabinta dokokin jam´iyar ta su, ta yada za ta taka rawar zamani.