SiyasaAfirka
Arangama da jami'an tsaro kan matakin dage zabe a Senegal
February 6, 2024Talla
A jiya Litinin ne 'yan majalisu 105 suka kada kuri'ar amincewa da kudirin yayin da wani dan majalisa daya ya nuna kin amincewarsa, bayan jami'an tsaro sun fitar da 'yan adawa daga cikin majalisar ta hanyar amfani da karfi.
Wannan mataki dai, na nufin share fage ga Shugaba Macky Sall da ke neman kasancewa a kan madafun iko har sai an samar da wanda zai gaje shi da ya amince da shi.
Wannan dai shi ne karon farko da kasar Senegal ke jinkirta zaben shugaban kasa, kuma tuni 'yan adawa suka yi watsi da matakin kai zaben watan Disamba tare da kiran magoya bayansu da su fito don nuna adawarsu. An katse kafar Intanet da ma dakatar da wata kafar yada labarai ta talabijin da hukumomin Dakar suka zarga da ingiza al'umma.