1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta yanke huldarta da kasar Ukraine

August 7, 2024

Hukumomin kasar Nijar sun sanar da dakatar da huldar diflomasiyya da Ukraine a kan abin da ya shafi harin 'yan tawaye da ya auku a kasar Mali a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4jBnU
Shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abourahmane Tiani
Shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abourahmane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin soja a Nijar, ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Ukraine saboda wasu kalaman da suka fito daga bakin wasu jam'ian Ukraine din da suka goyi bayan kungiyoyin da suka kai farmaki a Mali.

Harin dai da ya yi sanadin mutuwar sojoji Malin da na kamfanin Wagner na kasar Rasha.

Matakin Nijar na yanke hulda da Ukraine dai ya biyo makamancinsa da kasar Mali ta yi dangane da goya wa mayakan tawaye baya da ya yi sanadin mutuwar sojojin a a karshen watan jiya.

Sojojin hayar Rasha 84 ne dai bayanai ke tabbatar da cewa suka mutu a lamarin, yayin da Mali ta rasa nata mayaka su 47.

Lamarin ya kuma kasance gagarumar asarar da kamfanin Wagner ya gani cikin shekaru biyu da ta kai dauki Mali da nufin yaki da kungiyoyin mayakan tarzoma.