Jama'ar Timbuktu ta jinjinawa ICC
September 27, 2016Alkalai a kotun hukunta man'yan laifuka na kasa da kasa da aka sani da ICC, sun samu Ahmad al-Faqi al-Mahdi, da laifin rusa masallatai da wuraren ajiye kayan tarihin addinin Islama, wanda aka kyasta tarihinsa ya faro ne tun karni na 15. A lokacin da 'yan ta'adda suka mamaye arewacin Mali, sun yi amfani da motocin rusau da diga wajen rusa wuraren tarihin. A martaninsa Mohamed Issa Toure, wani matashi da ke zama a birnin Timbuktu, ya ce ya gane wa idanunsa lokacin da 'yan ta'adda ke rushe-rushen a wacan lokacin. Ya ce al-Mahdi a lokacin ya dauki kansa tamkar wani fir'auna, amma a yau an nuna masa, shi ba komai ba ne a duniya, kuma gashi zai shiga gidan yari. Ita ma dai kungiyar kula da al'adu ta MDD wato UNESCO ta yi maraba da hukuncin da aka yanke, wanda shi ne hukunci irinsa na farko a tarihi bisa rusa wuraren adana kayan tarihi.