Jama'a na fama da karancin kanazir a Kamaru
October 20, 2023Biranen Yaoundé da Douala a Kamaru sun shiga kwanaki na uku a jere suna fama da karancin kananzir hakan ya sa farashin sa ya tashi daga CFA 410,19 zuwa 560,19 a kasuwanin bayan fage
Kawo yanzu al'umma na ci gaba da kokawa sakamakon rashinsa, suna kwashe sa'o'i da dama suna jiran a biya musu bukata, man kananzir ya zama tamkar lu'u-lu'u a kasar.
Wani ma'aikancin gidan burodi ya kwashe kwanaki da dama yana neman kananzir ruwa a duk fadin Yaounde da kewaye amma bai samu ba
Hakan ya sanya 'yan kasuwar kananzir a bayan fage suka kara farashi ba bisa ka'ida ba ga mabukata wanda ya jefa su cikin halin kakani ka yi, duk da matatar man fetur da kasar ke da ita, al'umma na shan wahala kuma hakan bai dace ba inji Yarima Ousmanou Haouna masanin tattalin arziki a kasar
"Ya ce a gaskiya al'umma sun shiga halin kakani ka yi, kasancewar mu a kasar Kamaru muna da matatar man fetur mai zaman kanta ta kasa mai suna Sonara da ke Limbe, shi ya sa bai kamata a ce an rasa kananzir ba, saboda muna da man fetur a Kamaru abin mamaki gwamnatin ta yi biris kamata ya yi a ce gwamnati ta fito ta yi wa mutane bayani"
Al'umma a Kamaru dai sun fara shiga rudani yayin da sabon farashin man ya fara aiki ranar daya ga watan Fabairun da ya gabata bayan da gwamnatin kasar ta sanar da janye tallafin da ta ke bayarwa a farashin man fetur, matakin da ya kai ga tashin mai da kashi 15 cikin 100, saboda matsin lamba daga asusun bada lamuni na Duniya IMF.
Sai dai daga bisani gwamnatin ta ware wani kaso daga cikin kudaden da ta janye domin daukar matakai da suka hada da na rage farashin man kananzir da gas na girki sakamakon karin albashi da kashi 5.2 cikin 100 da aka yi wa ma'aikatan gwamnati amma kawo yanzu ba a rage farashin kananzir din ba a gidajen mai.
A Najeriya ma tsugunne ba ta kare ba ga al’ummar shiyyar Arewa maso gabashin kasar bayan da aka fara fuskantar karancin man fetur a gidajen mai a jihohin shiyyar abin da ya haifar da fargaba da karuwar tsadar rayuwa da kuma tsadar abinci.
Sai dai kamfanin albarkatun mai na NNPCL na kasar ya nemi jama'a su kwantar da hankulansu su daina fargaba akwai isasshen mai da al’umma za su iya saya su yi amfani da shi.