Jagoran 'yan awaren kamaru gaban kotu
November 1, 2018Jagoran 'yan awaren yankin da ke amfani da Turancin Ingilishin kasar Kamaru Sisiku Julius Ayuk Tabe wanda mahukuntan Najeriya suka kama a watan Janerun da ya gabata suka mika wa mahukuntan Kamaru ya bayyana a karon farko tun bayan kamunsa a wannan Alhamis a gaban kotun a birnin Yaounde shi da wasu 'yan awaren su tara.
Jagoran 'yan awaren kasar ta Kamaru ya bayyana ne a gaban kotun domin sanin makomarsa a game da bukatar neman belinsa da lauyoyinsa suka shigar a gaban kotun.
Watanni 10 kenan dai rabo da a ga jagoran 'yan awaren yankin Ambazoniyar kasar ta Kamaru mai shekaru 46 a bainal jama'a ba, lamarin da ya jefa danginsa cikin fargabar makomarsa a hannun mahukuntan kasar ta Kamaru. Daga karshen zaman na yau dai kotun birnin na Yaounde ta tsaida ranar 15 ga watan Nowamba domin bayyana matsayinta a game da bukatar belin nasa.