Jagoran hamayya a Sira'ila ya yi kiran shiga yajin aiki
September 1, 2024Jagoran adawa a siyasar Isra'ila, Yair Lapid ya yi kiran da a shiga yajin aiki a fadin kasar, domin matsa wa gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu lamba domin ta nemo yadda za ta yi na ganin an sako 'yan kasar da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza.
Mr. Lapid wanda shi ne tsohon Firaminista ne a Isra'ilar, ya ce lokaci ya yi da za a dauki matakin toshe fannin tattalin arzikin kasar domin tilasta gwamnati daukar mataki.
Musamman ya bukaci dukkanin dan mai kishin ci gaban Isra'ila da su fito a yau Lahadi domin gangamin a birnin Tel Aviv.
Kalaman Mr. Lapid sun kuma zo ne bayan gano gawarwakin wasu daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su, yana mai cewa yajin aiki ne kadai zai iya kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas.
Jagoran adawar ya kuma yi kira da babbar murya ga shugabannin kwadago da sauran kungiyoyin 'yan kasuwa da su shiga yajin aikin ba tare da wani bata lokaci ba.