Italiya da Libiya sun dawo da sufurin jiragen sama
September 30, 2023Talla
Hukumomi a Libiya na cewa tuni jirgin MT522 na kasar ya tashi daga filin jirgin sama na birnin Tripoli zuwa birnin Rome. Ana kuma sa ran ya sake dawowa Tripoli a wannan Asabar din. A yanzu dai kasashen biyu sun cimma matsayar cewa, kamfani guda na jirgin sama zai rika zirga-zirga tsakanin biranen biyu.
Italiya dai da wasu kasashen yammacin Turai sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Libiya da ke arewacin Afirka tun bayan kisan tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi a shekarar 2011.
Karin bayani: Libya: Shekaru 10 bayan kifar da Ghaddafi
Dama dai a watan Yulin wannan shekarar ce, firanministar Italiya Giorgia Meloni ta sanar da dage takunkumin sufurin da kasar ta kakabawa Libiya.