1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari a iyakar Labanan da Syria

November 30, 2024

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai farmaki wata cibiyar soji da ke iyakar Labanan da Syria, wajen da a cewarta mayakan Hezbollah ke amfani da shi wajen safarar makamai.

https://p.dw.com/p/4nbaG
Hare-haren Isra'ila a kan iyaka
Hare-haren Isra'ila a kan iyakaHoto: IBRAHIM AMRO/AFP

Isra'ila dai ta zargi kungiyar ta Hezbollah da saba yarjejeniyar tsagaita wuta wajen amfani da wannan kafa ta fasa kwaurin makaman daga Syria.

Haka ma sojojin na Isra'ila sun ce suna gudanar da bincike a kudancin Labanan, inda cikin sa'o'in da suka gabata ta gano makamai da aka boye a wani masallaci.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.

Yana daga cikin abin da yarjejeniyar ta kunsa, sojojin Labanan da na Majalisar Dinkin Duniya za su kasance a kudancin, inda su kuwa daga nasu bangaren sojojin Isra'ila za su janye na tsawon kawanaki 60.

Bangarorin biyu na zargin juna da saba yarjejeniyar.