1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun sakar Isra'ila da Hezbollah

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
September 2, 2019

An yi musayar wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah a kan iyakar Lebanon da Isra'ila, abin da ke haddasa fargabar barkewar sabon rikici a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3Orxn
Libanon Israel Artillerie Beschuß
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe tsawon makwanni ana zaman tankiya tsakanin bangarorin biyu, abin da ke sanya damuwa ga kasashe masu fada a ji a duniya. 

Isra'ilan dai ta bayyana cewa ta harba kimanin makaman atilare 100 bayan da kungiyar ta Hezbollah ta harba wasu makamai masu linzami na kariya daga hare-hare guda biyu zuwa uku a shalkwatar rundunar sojojin Isra'ilan, abin da kuma ya shafi motar daukar marasa lafiya ta sojojin.

Sai dai Isra'ilan ta musanta ikirarin da Hezbollah ta yi na cewa ta kashe sojojinta da ke cikin motar, tana mai cewa babu wanda ya samu koda kwarzane. Firaministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu ya ce suna jiran mataki na gaba da za su dauka kan Hezbollah din.