Isra'ila da Gaza sun kasa tsagaita wuta
May 11, 2023Jiragen yakin Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a sassan birnin Gaza da yankin Khan Yunus, a matsayin martani ga ruwan rokoki da ake harba musu daga yankin Falalsdinawa. Isra'ila ta ce rokokin sun kai dubu uku, amma ta kakkabo kusan rabinsu a yayin da sauran suka fada dazuka da gidajen jama'a da gonakai dama kan tituna, lamarin da ya kai ga bude ramukan buya don kariya daga tashin hankali.
Tun da fari dai, matakin kisan dauki dai-dai da Isra'ila ta dawo aiki da shi a wani halin kwantan bauna da rokoki da jiragen sama kan gidansu, shi ne musabbabin barkewar ba ta kashin da Firaministan Isra'ila ya suffanta da shiga halin yakin da ba a san karshensa ba. Wannan ne ya kai ga kashe manyan kwamandodin kungiyar Islaminc Jihad mai fafutukar neman 'yanta Falalsdinu da karfin tuwo da iyalansu 12,
Isra'ila ta sha alwashin murkushe makiyanta
Benjamin Netanyahu ya ce: "Ya ku 'yan Isra'ila, ina sanar muku da cewa, a halin yanzu muna ci gaba da ragargazar mabuyar 'yan ta'addan da ke neman ganin bayanmu. Mun shiga cikin halin yakin da ko mu yi nasara ko makiyanmu su cimma mana. Ina kara jaddada cewa, a duk lokacin da 'yan ta'adda suka takale mu, to za su dandana kudarsu."
Sai dai Izhaq Levy, dan majalisa na jam'iyyar adawa ya soki Netanyahu kan neman karkata hankalin 'yan isra'ila zuwa ga yaki da Zirin Gaza don karya lagon zanga-zangar adawar da ake da shi. Sannan ya suffanta matakin Firaminista Netanyahu da dawo da kisan dauki dai-dai kan jagororin Falalsdinawa da ba zai haifar wa Isra'ila ci-gaba ba.
Levy ya ce: "Idan za mu yi dogon tunani, za mu tabbtar da cewa, irin wannn matakin 'yan gada-gadan da babu lissafi a cikinsa, zai kara shafa wa kasarmu ta Isra'ila kashin kaji ne. A maimakon Netanyahu ya ba wa masu zanga-zangar adawa da shi amsa ta amincewa ya gurfana a gaban kotu, ya soke dokar da ta yi matukar raba kan 'yan Isra'ila. A yanzu yana son huce haushinsa kan Zirin Gaza da sunan yaki da ta'adancin da mun jima da murkusheshi."
Hamas ta ce babu gudu babu ja da baya
Kungiyar Hamas tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyin gwagwarmaya sun ce wa Isra'ila cewar, taba daya daga cikinsu tamkar taba dukkanin al'ummar Falalsdinu ne, saboda haka da ba za ta taba yin shiru ba, za ta mai da mummunan martanin ramuwa a ko yaushe a kuma ko'ina.
Isma'il Haniyeh, shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai, ya sanar da shirin kungiyarsa na shiga yakin sai baba ta gani da Isra,ila, inda ya ce: "A yau mutanen Gaza na sanar da ku cewa, wannan fito na fiton da muke yi da Isra'ila, fafutuka ce ta ko a mutu ko a yi rai. Dukkanimu a shirye muke mu kwanta dama don kare mutuncin al'umarmu da dauko fansar rayukan shahidanmu gami da fafutukar 'yanta masallacin Al-Aqsa dama Falasdinu."
Kasashen Masar da Katar da Jordan dama Amirka na ci gaba da tuntubar bangarori biyun don mayar da wukakensu kube da nufin kauce wa aikata duk wasu matakan dagula lamura a yankin Gabas ta Tsakiya.