IS ta kai hari a barikin soji a Libiya
May 4, 2019Talla
Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wani hari a barikin soja da ke garin Sebha na kudancin kasar Libiya wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji guda tara a sanyin a safiyar wannan Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito magajin garin Sebha Hamed al-Khayali na cewar an kai farmakin ne da hadin bakin wasu sojojin haya 'yan ta'adda tare da kashe sojojin wasunsu bayan da aka yi masu yankan rago, kana kuma maharan sun saki daukacin fursunonin da ke daure a cikin gidan yarin barikin.
Tun da jimawa dai garin na Sebha da ke lardin Sebhana ya fada hannun madugun yaki Khalifa Haftar a yunkurinsa na karbe mulki a hannun gwamantin hadin kan kasar mai goyon bayan manyan kasashen duniya.