1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta hari Kurdawan Iraki da makami mai guba

Gazali Abdou TasawaFebruary 26, 2016

Shugabannin Kurdawa Iraki sun zargi Kungiyar IS da harar mayakan kungiyar ta su da makami mai guba a tsakiyar wannan mako a Arewa maso Yammacin Iraki.

https://p.dw.com/p/1I3CL
Kurdische Sicherheitskräfte Peschmerga Irak
Hoto: picture-alliance/dpa/A.Zangana

Shugabannin Kurdawa Iraki sun zargi Kungiyar IS da harar mayakan kungiyar tasu da makami mai guba a tsakiyar wannan mako a Arewa maso Yammacin Iraki.Shugabannin Kurdawan Arewacin Irakin sun ce za su kaddamar da wani bincike domin hakikance nau'in makamin da Kungiyar ta IS ta yi amfani da shi kan mayakansu na Peshmergas.

A wani sako da ya wallaha kan shafinsa na Tweeter kwamitin tsaro na Kurdawan Irakin ya ce gwamman mayakansa dama wasu fararan hula na yanki ne aka kontar da su a assibiti bayan da suka yi ta fama da amay biyo bayan wani harin roka da yake zaton na dauke da sinadari mai guba da Kungiyar ta IS ta kaddamar a yankin Sinjar a ranar 25 ga wannan wata na Fabrairu.