1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

IOM ta ce akwai karin hadarin samun mace-mace a Sudan

August 14, 2024

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM, ta yi kira ga kasashe da su cika alkawuran da suka dauka na tallafa wa Sudan, wadda ke fama da matsanancin matsaloli na yaki da ke bukatar jinkai.

https://p.dw.com/p/4jR74
Hoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Hukumar ta IOM dai na gargadin cewa jan kafa wajen taimaka wa Sudan na iya zama sanadin mutuwar dubban rayukan fararen hula cikin watanni masu zuwa.

Kawo i yanzu a cewar hukumar, kaso 21% ne na tallafin da kasashen duniya suka yi alkawari aka iya samarwa ga kasar kuma da ke cikin tsananayin yanayi na bukatar dauki.

Kasar Sudan da ke fama da yaki, na cikin hali na yunwa da cututtuka gami da ibtila'in ambaliya.

Sama da mutum miliyan 10 ne dai suka rasa gidajensu a Sudan, yayin da fiye da miliyan biyu suka bar kasar baki daya.