1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Indiya sun koma rumfunan zabe

Zainab Mohammed Abubakar
May 12, 2019

Mutane sun fara kada kuri'unsu a zagayen kusa-da-na-karshe na zabukan kasa baki daya da 'yan adawa suka lashi takobin hana framinista Narendra Modi samun damar zarcewa a karo na biyu a Indiya

https://p.dw.com/p/3IMZX
Indien Westbengalen Wahl
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Das


Sama da Indiyawa miliyan 100 a fadin jihohin kasar bakwai nedai, suka cancanci kada kuri'unsu a zagaye na shida, na zaben da ke daukar tsawon kwanaki 39 a na gudanarwa, wanda Modi ya kaddamar a ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata.

Zabukan Indiyar na zuwa ne bayan kashe wutar sabbin rigingimu da suka barke tsakanin kasar da makwabciyarta Pakistan. 

Jam'iyyun adawa da ke hasashen rashin nasarar jam'iyyar framinista Modi ta 'yan Hindu, sun fara tattauna hadaka don kama madafan iko, idan aka kammala zabukan a ranar 19 ga watan Mayu.

Kidayar kuri'un zai fara ne a ranar 23 ga wannan wata na Mayu