1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inda kasa mafi yawan al'uma a duniya

Abdourahamane Hassane
April 19, 2023

Ana sa ran Indiya za ta zama kasa mafi yawan jama'a a duniya nan da tsakiyar wannan shekara , inda za ta zarce China da kusan mutane miliyan uku.

https://p.dw.com/p/4QJrN
Indien Symbolbild Bevölkerungsdichte
Hoto: Rafiq Maqbool/AP/picture alliance

A cikin wani rahoton da ta bayyana hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar Dinkin Duniya  UNFPA ta ce ya yawan al'ummar na Indiya zai kai biliyan 1. Da miliyan dubu hudu da yan ka a tsakiyyar wannan shekara. Bisa kididdigar da aka fitar a farkon wannan shekarar, yawan jama'ar kasar China ya ragu a shekarar da ta gabata a karon farko tun daga shekarar 1960, bayan wata yunwa da ta afku, wacce ta yi sanadin mutuwar dubun-dubatar miliyoyin mutane.