1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya za ta kara kudin fito ga Amirka

Yusuf Bala Nayaya
June 14, 2019

Kokarin da Amirka ke yi na kawo karshen kulawa ta musamman da kayan kasuwanci na Indiya abu ne da dama an tsammaci zai haifar takun saka ta fuskar kasuwanci tsakanin Indiya da kasar ta Amirka.

https://p.dw.com/p/3KUHc
Symbolbild: Handel USA Türkei Indien
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Wüstneck

Kasar Indiya ta mayar wa Amirka da martani kan harajin kayan fito na wasu kayayyakinta da suka kai 20, wadanda ake shiga da su Indiya daga Amirka, wani jami'in gwamnati ya bayyana haka a wannan Juma'a, abin da ke zuwa bayan da mahukuntan birnin Washington suka janye wata moriya da Indiyar ke samu a harkokin kasuwanci da Amirka a wannan wata.

Kokarin da Amirka ke yi na kawo karshen kulawa ta musamman ga kayan kasuwanci na Indiya ke samu idan za su shiga kasar Amirka daga ranar biyar ga watan Yuni, wani abu ne da dama an tsammaci zai haifar takun saka ta fuskar kasuwanci tsakanin Indiya da kasar ta Amirka.

Nan gaba a wannan rana ce dai za a bayyana irin kayayyaki na Amirka da za a maka wa karin kudin fito kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasuiwanci a Indiya ta bayyana.