Indiya: Hukuncin kisa kan wani mai fyade
May 12, 2018Talla
Kotun da ke birnin Madhya Pradesh a jihar Idore ta ce ta yanke wannan hukunci ne duba da irin nauyin laifin da mutumin mai shekaru 21 da haihuwa ya aikata kuma hakan zai zama izina ga sauran jama'a.
Cikin makonni uku kacal ne kotun ta kai ga yanke wannan hukunci wanda shi ne mafi sauri da aka yi a kasar ta Indiya wadda sassanta da dama ke fama da matsaloli na cin zarafin mata ta hanyar lalata, lamarin da ke cigaba da jawo tada hankalin al'ummar kasar musamman mata.