Indiya ta kori 'yan gudun hijirar Rohingya
October 5, 2018Mutanen bakwai na daga cikin dubban 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikicin kabilanci suka kuma nemi mafaka a Indiya, hukumomin Indiyan sun kin amincewa da bukatarsu ta neman mafaka duk da barazanar rasa rayukansu da suka ce za su fuskanta muddun aka tilasta musu komawa gida.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki wannan mataki, inda ta ce bai kamata a yi facali da barazanar da rayuwar wadannan mutanen ke ciki in har sun koma gida ba. An dai dauki matakin ne bayan da kotun da aka shigar da koken mutanen gabanta ta yi fatali da bukatar ba su mafaka, akwai zargin da ake wa wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka da ra'ayi irin na masu tsatsauran ra'ayin addini da Indiyan ke ganin barazana ce ga tsaron kasa.