Indiya ta kare matsayinta bisa sauyin yanayi
December 5, 2014Prakash Javadekar mai fafutukar kare muhalli ya fadawa manema labarai a birnin New Delhi cewa, ba za su mika wuya ba kan duk wani abu da zai iya kawo zagon kasa ga ci gaban kasarsu.
Indiya ta bayyana wannan matsayin ne a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya a Lima babban birnin kasar Peru, ta ce yunkurin na iya kawo nakasu ga ci gaban da ta ke samu, ya kuma kawo cikas ga fafutukar da ta ke yi na yaki da talauci a tsakanin al'ummarta.
Da yake jawabi yayin da yake barin taron na birnin Lima, Prakash Javadekar tsohon dan majalisa kuma mai fafutukar kare muhalli a kasar ta Indiya ya ce, ya je taron zuwa zuciyarsa a bude kuma ya gargadi tawagar Indiya cewa kasarsu ba zata daga kafa ba ko jin kunya idan za a zauna teburin zazzafar muhawara.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman