1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta haramta fitar da farar shinkafa

July 21, 2023

Indiya da ta fi kowace kasa fitar da shinkafa a duniya ta sanar da haramta fitar da shinkafa zuwa kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/4UD9Z
Hoto: ILNA

Ana ganin matakin gwamnatin Indiya zai haifar da farashin shinkafa ya kara tashin gwauron zabi. Ma'aikatar samar da abinci ta kasar ta ce, Indiya ta hana fitar da duk wata farar shinkafa da ba Basmati ba domin dakile karancinta da ma tashin farashinta a kasuwannin cikin gida. Kasashen da haramcin fitar da shinkafar daga Indiya zai shafa sun hada na nahiyar Afirka da Turkiyya da Siriya da kuma Pakistan da dama suke fama da tsadar farashin kayan abinci.

Ko a bara, Indiya da ke safarar fiye da kashi 40 na shinkafarar duniya, ta hana fitar da alkama da kuma siga saboda daidaita farashinsa a kasar. An dai ga yadda farashin shinkafar kke tashi a kasuwannin duniya sakamakon annobar Corona da tasirin yakin Ukraine da na sauyin yanayin na El nino.