1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta fuskanci girgizar kasa mai karfi

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 4, 2016

Mutane biyar sun muta a wata girgizar kasa mai karfi da ta afku a Indiya, yayin da wasu karin mutane 100 suka jikata.

https://p.dw.com/p/1HXUX
Indien Erdbeeben in Imphal
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Raj

Wata girgizar kasa mai karfin maki shida da digo takwas a ma'aunin Richter ta afku a Imphal da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar Indiya da asubahin wannan Litinin. Alkaluman da hukumar 'yan sandan kasar ta fitar sun nunar da cewar akalla mutane biyar sun rasa rayukansu ya zuwa yanzu yayin da wasu karin 100 kuma sun jikata.

Gidaje da dama na garin Imphal da ya kunshi mutane dubu 270 sun lalace. A yanzu haka dai jami'an jin kai na kai agajin gaggawa tare da tono mutanen da baraguzan gine-gine suka binne.

Wani jami'an jinya ya ce " ina gida lokacin da girgizar kasar ta afku. Amma da ya ke ni ba abin da ya sameni, sai na hanzarta fitowa don kula da wadanda suka samu raunuka."

Rahotanni sun nunar da cewar an ji karfin wannan girgizar kasar a kasashen Bangladesh da Bama da Kuma Nepal. Dama garin Imphal na Indiya na da iyaka da kasar Bama ko Myammar.