1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Ana kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokoki

Abdourahamane Hassane
April 11, 2019

An bude rufunan zabe a Indiya inda ake gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki wanda ake sa ran mutane miliyan 900 wadanda suka cancanci yin zaben za su kada kuri'a domin zaben 'yan majalisu 543.

https://p.dw.com/p/3GafS
Indien Wahlen
Hoto: DW/Suhail Waheed

Firaministan mai barin gado Narendra Modi dan kabilar Hindu na jami'yyar BPJ wanda ya kammala wa'adin farko na mulki na shekaru biyar na fuskantar kalubale a zaben daga abokin hamayarsa Rahul Ghandi.