1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Na shirin daukar matakai kan ababen hawa

Binta Aliyu Zurmi
November 4, 2019

Hukumomin birnin New Delhi za su bullo da wani shirin rage yawan ababen hawa da ke yawo a kan tituna.

https://p.dw.com/p/3SRHO
Indien: Umweltbelastung und Luftverschmutzung in Neu-Delhi
Hoto: Getty Images/AFP/X. Galiana

Tsarin wanda za a dauki makonni biyu ana yinsa, zai gudana ne ta hanyar la'akari da lambobin motoci masu zaman kansu da kuma na 'yan kasuwa, inda za a ba da wasu kwanakin ga wani rukuni, sannan wani rukunin ya biyo.

Akalla akwai motoci dubu 150 da aka haramta wa hawa hanoyoyi a yau Litinin, inda duk wanda aka samu da laifin taka dokar, ka iya biyan tarar rupee 4000 na kudin kasar kwatankwacin dalar Amirka 57.

Yanayin iska a birnin na Delhi dai na ci gaba da tabarbarewa sakamakon yawan ababen hawa, inda hukumomin da ke kula da al'amarin ke cewa ya mai kai maki 490, wanda hadari ne matuka ga lafiyar jama'a.