1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabiyar Indiya ta mutu tana da shekaru 92

Ramatu Garba Baba
February 6, 2022

Shaharrariyar mawakiyar Indiya Lata Mangeshkar ta mutu tana da shekaru 92 a duniya. Zabiyar ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Mumbai bayan ta kamu da corona.

https://p.dw.com/p/46ajX
Lata Mangeshkar Sängerin Indien
Hoto: Dinodia Photo/imago images

Al'ummar Indiya da ma masoyan wakokin Indiya ne ke jimamin mutuwar shahararriyar zabiyar kasar Lata Mangeshekar da ta mutu a daren a wannan Lahadin tana da shekaru casa'in da biyu a duniya.

Lata Mangeshrekar ta shahara sosai a ciki dama wajen Indiya, ta mutu ne a wani asibiti da ke a birnin Mumbai bayan ta shafe sama da makonni uku tana jinyar cutar corona. Firaiminista Narendra Modi ya baiyan alhininsa inda ya ce, Indiya tayi babban rashin da ba me iya maye gurbinta.

Tuni Gwamnatin Indiya ta aiyana zaman makoki na kwanaki biyu tare da sauke tutar kasar don karrama zabiyar, sanarwar gwamnatin ta ce, ana cikin shiri don yi mata jana'iza irin ta ban girma.